Home Labaru Kasuwanci Kasuwanci: Nijeriya Za Ta Fara Sayarwa Kasar Indiya Mai

Kasuwanci: Nijeriya Za Ta Fara Sayarwa Kasar Indiya Mai

661
0
Satar Mai: Nijeriya Ta Yi Asarar Bilyan 17 Cikin Watanni 5 – NNPC
Satar Mai: Nijeriya Ta Yi Asarar Bilyan 17 Cikin Watanni 5 – NNPC

Shugaban rukunin kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, Mele Kyari ya ce zai fara sayarwa kasar Indiya kashi goma na man fetur.

 Kyari ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a lokacin da wakilin Indiya, Abhay Thakur ya kai ziyara a hedikwatar NNPC a Babban Birnin Tarayyar Abuja.

Shugaban rukunin kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, Mele Kyari

A cewar Mele Kyari kamfanin ya yi hakan ne don taimakawa Indiya ta warware matsalar makamashi da ta ke fama da shi.

Indiya dai ita ce ta biyu a duniya  ma fi yawan jama’a kuma tana bukatar man fetur daga wasu kasashe don warware matsalar makamashi da take fama da ita a halin yanzu.

Mele Kyari, ya ce Nijeriya za ta ci gaba da tallafawa Indiya wurin warware matsalar da take fama da ita ta kowacce hanya da za ta iya.

Ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar fahimatar juna da Najeriya da Indiya suka rattaba hannu a kai za ta karfafa dangantaka tsakanin su.

Kyari ya kara da cewa, ce NNPC a shirye yake don yin hadaka  da Indiya don ganin kasashen biyu sun amfana da juna. mall”