Home Labaru Tsaro: Hukumar NSCDC Zata Tura Jami’ai 1500 Dazuka

Tsaro: Hukumar NSCDC Zata Tura Jami’ai 1500 Dazuka

732
0

Hukumar jami’an tsaron farin kaya ta Civil Defence ta kammal shirin tura jami’anta dazuka domin samar wa manoma da makiyaya tsaro daga hare-haren ƴan ta’adda.

Hukumar ta yi haka ne a ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya da ma’aikatan ayyukan gona mai suna ‘Agro Rancher Scheme’.

A ƙarƙashin shirin hukumar za ta tura ma’aikata 1,500 cikin dazuka domin daƙile ayyukan mahara da masu tada zaune tsaye a gonaki.

Shugaban hukumar, Abdullahi Muhammadu ne ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Barno.

Ya ce wannan shiri an tsara shi ne domin samar da tsaro a gonaki da wuraren da makiyaya ke kiwon su. Bayan haka aƙalla jami’ai 250 ne aka ƙeɓe domin wannan aiki a zangon farko.

Muhammadu ya ce hukumar za ta horas da ma’aikata 750 na tsawon makonni biyar kafin ta tura su.

Za a tura jami’an ne zuwa jihohin Katsina da wasu jihohin dake fama da ta’addancin maharan. f