Home Labarai Iftila’i: Gidaje Sun Kone Kurmus A Sanadiyyar Faduwar Tankar Mai A Ogun

Iftila’i: Gidaje Sun Kone Kurmus A Sanadiyyar Faduwar Tankar Mai A Ogun

21
0
Abuja tanker explosion
Abuja tanker explosion

Wata tankar mai ta kama da wuta bayan ta faɗi a garin Ibafo da ke ƙaramar hukumar Obafemi-Owode da ke jihar Ogun, inda gidaje da motoci da dama suka ƙone, sannan mutum biyu suka jikkata.


Lamarin ya auku ne a babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan, inda ganau suka ce tayar motar ce ta fashe, sai ta faɗi, inda tankin ya fashe wanda shi ne sanadiyar wutar.


Kakakin hukumar kula da sufuri da ababen hawa na jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da lamarin.


Shi ma kakakin rundunar sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce wutar ta kai har wani gidan mai mai suna Osadole, inda ta ƙona manyan motoci biyu da aka ajiye a waje

Leave a Reply