Home Labaru Ibtila’i: Yadda Rayuka Su Ka Salwanta Sakamakon Ruftawar Gini A Filato

Ibtila’i: Yadda Rayuka Su Ka Salwanta Sakamakon Ruftawar Gini A Filato

168
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato, ta tabbatar da mutuwar mutane uku, yayin da wasu da dama su ka samu rauni bayan ruftawar wani gini mai hawa biyu a birnin Jos na jihar Filato.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Litinin gabata ne, wani gini da ya kunshi shaguna da wuraren zaman jama’a ya rufta a Jos, lamarin da ya haifar da asarar dukiya da rayuka.

Duk da cewa har yanzu ba a san musabbabin rugujewar ginin ba, ‘yan sanda sun ce sun aika tawagar masu aikin ceto zuwa wajen domin taimaka wa wadanda abin ya rutsa da su.

Jami’in yada labarai na rundunar DSP Tyopev Mathias, ya ce da misalin karfe hudu na yammacin Litinin ne aka kira su domin sanar da su abin da ya faru, kuma ba su bata lokaci ba su ka garzaya zuwa wajen, inda su ka ceto mutane bakwai da ba su ji rauni ba..

Daga bisani masu aikin ceto su ka sake fito da wasu mutanen da su ka jikkata aka kai su asibitin Kwararru da ke Filato da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bingham domin a duba su.
������ ���