Home Labaru Martani: Buhari Da Obasanjo Sun Fi Kowa Sanin Kan Su – Shehu...

Martani: Buhari Da Obasanjo Sun Fi Kowa Sanin Kan Su – Shehu Sani

184
0
Sanata Shehu Sani, Dan Majalisar Dattawa
Sanata Shehu Sani, Dan Majalisar Dattawa

Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya ce ya tuna da yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya caccaki Obasanjo a bainar jama’a lokacin da ya ke a matsayin Shugaban kasa.

Shehu Sani ya bayyana haka ne, yayin da ya ke maida martani game da kumfar bakin da mutane ke yi a kan wasikar da Obasanjo ya aike wa shugaba Buhari dangane da halin da Nijeriya ke ciki.

Tsohon sanatan ya kuma roki shugaba Buhari da cewa, ya dubi wasikar Obasanjo da idon basira, ya na mai cewa da Obasanjo da shugaba Buhari sun san kan su fiye da yadda wani ya san su.

Obasanjo dai ya sake aike wa shugaba Muhammadu Buhari wasika, inda ya ke gargadin cewa Nijeriya ta na cikin halin Ha’ula’i kuma shugaba Buhari ne kadai ke iya ceto ta. ������6�s