Home Labaru Kurungus: ‘Yan Sanda Sun Kama Makasan Funke Olakunrin A Jihar Ondo

Kurungus: ‘Yan Sanda Sun Kama Makasan Funke Olakunrin A Jihar Ondo

203
0

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo Mista Femi Joseph, ya ce an kama ‘yan ta’addan da ake zargin su ne makasan ‘yar shugaban kungiyar Yarbawa ta Afenifere Funke Olakunrin.

A cewar sa, gamayyar jami’an tsaro masu sintiri ne su ka afka cikin daji a Ore da ke jihar Ondo su ka samu nasarar kama ‘yan ta’addan.

Sai dai Kakakin ya ce ba a bayyana fuskokin su ba, amma za a yi hakan ba da dadewa ba, yayin da ake ci-gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

A nata bangaren dai, Kungiyar Fulani Makiyaya ta Nijeriya MACBAN, ta yi Allah-Wadai tare da nesanta kan ta daga kisan Funke Olakunrin.