Home Labarai Hukumar EFCC Ta Gurfanar Da Janar Na Sojan Bogi a Kan Damfarar Miliyoyi

Hukumar EFCC Ta Gurfanar Da Janar Na Sojan Bogi a Kan Damfarar Miliyoyi

82
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta gurfanar da
wani mai mukamin janar na sojin kasa na bogi mai suna Bolarin
Abiodun a gaban mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na kotun
musamman da ke Ikeja a Legas.

An dai gurfanar da Bolarin a kan tuhume-tuhume goma sha uku,
wadanda su ka hada da zamba da karya da mallakar takardun
bogi da damfarar Naira miliyan dari biyu da sittin da shida da
dari biyar.

Wanda ake tuhumar dai ya bayyana kan sa a matsayin Janar na
sojin kasa, inda ya zambaci kamfanin Kodef Clearing Resources
da cewa shugaba Buhari ya zabe shi a matsayin shugaban
rundunar sojin kasa kuma ya na bukatar wasu kudade domin
cimma burin sa.

An da kama Bolarin ne a gidan sa da ke Alagbado a jihar Legas,
inda aka same shi da takardun bogi da su ka hada da shaidar
kama aiki a matsayin shugaban rundunar sojin kasa da shugaba
Buhari ya sanya wa hannu.