Home Labarai Zaben Katsina: APC Ta Lallasa PDP, Ta Lashe Dukkan Kujeru 31

Zaben Katsina: APC Ta Lallasa PDP, Ta Lashe Dukkan Kujeru 31

334
0

Jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujeru 31 a zaben kananan
hukumomi da aka gudanar a jihar Katsina.

Babban sakataren hukumar zabe ta jihar Alhaji Lawal Faskari ya
sanar da haka a Katsina, sai dai ya ce ba a kammala zaben ba a
kananan hukumomin Daura da Funtua.

Lawal Faskari ya kara da cewa, an soke zabe a karamar hukumar
Dutsin-Ma saboda wasu kalubale, ya na mai cewa an yi zaben
cikin lumana a duk sauran yankunan.

Ya ce ya zuwa yanzu hukumar ta karbi cikakken sakamako daga
kananan hukumomi 31, da gundumomi 328, yayin da ta ke jiran
na Funtua da Daura sannan an soke zabe a Dutsin-Ma.

Leave a Reply