Home Labarai Martani: Motoci Kirar Cardillac 17 Mu Ka Ba Sarakuna Ba 230 Ba...

Martani: Motoci Kirar Cardillac 17 Mu Ka Ba Sarakuna Ba 230 Ba – Matawalle

40
0

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya maida martani a
kan cece-ku-cen da ya biyo bayan raba wa sarakunan gargajiya
motoci, da kuma alakanta sayen motocin da zunzurutun kudin da aka kiyasta ya kai biliyoyin naira.

Wasu ‘yan Nijeriya dai sun nuna rashin gansuwa da lamarin
raba wa sarakunan motocin, yayin da wasu ke ganin hakan a
matsayin taimaka wa sarakunan ne saboda da rashin tsaro da su
ke yawan fuskanta.

Tunda labarin raba motocin sama da 200 kirar Cardillac da aka
kera a shekara ta 2019 ga sarakunan ya karade kafafen sada
zumunta, ‘yan Nijeriya daga shiyoyi da dama ke ci-gaba da tofa
albarkacin bakin su a game da lamarin.

Wasu ‘yan Nijeriya sun yi ta bada misali ga labarin raba karin
motoci ga cibiyar tsaro ta yammacin Nijeriya, wanda aka fi sani
da suna Amotekun da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi,
inda ake cewa bai kamata jihar da ke fama da tarin matsalolin
tsaro ta raba motoci masu tsada ga sarakunan ba.

Sai gwamna Matawalle ya ce motoci 17 ne ya raba ba 200 ba,
kuma sarakunan da aka bamotocin an tabbatar da cewa ba su
hulda da ‘yan ta’adda.