Hukumar Bunkasa Arewa maso Gabas NEDC, za ta gina makaranta a garin Gashuwa da ke Karamar Hukumar Bade.
Hukumar tace za’a gina makarantar ne domin inganta harkokin
ilimi a yankunan da suka yi fama da rikicin Boko Haram.
Shugaban hkumar Alhaji Mohammed Alkali da kuma Gwamnan
Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni da Shugaban Majalisar
Dattawa, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ne suka kaddamar da
aikin gina makaranta ta farko.
A jawabin Babban Manajan Hukumar, ya ce Jihar Yobe ce ta
farko da za ta fara amfana da irin wannan aiki na gina
makarantar boko ta zamani.
A cewarsa da irin wannan ci gaba Jihar Yobe a yanzu ta kasance
jihar da ke kan gaba wajen cika sharuddan da hukumar take
bukata domin amfana da irin ayyukan hukumar.
A kwanakin baya Gwamna Buni da hadin gwiwar Hukumar
NEDC sun aza tubalin gina gidaje 500 a garin Damaturu wanda
shi ne na farko a wannan yanki da Hukumar NEDC za ta aiwatar
bayan kaddamar da gina hanyar Gujba zuwa Mutai.
You must log in to post a comment.