Home Labarai Ganduje Ya Bukaci Majalisar Tarayya Ta Hana Bara A Kan Tituna

Ganduje Ya Bukaci Majalisar Tarayya Ta Hana Bara A Kan Tituna

23
0

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya ce lokaci ya yi da ya kamata Majalisar Tarayya ta hana barace-barace a ko’ina a fadin kasar nan.


Gwamnan ya koka kan yadda iyaye ke tura ’ya’yansu yawon
barace-barace a kan tituna, lamarin da ya ce hakan rashin imani
ne.


Kiran na zuwa ne a yayin Taron Kasa karo na biyu wanda
Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Bayero Kano ta shirya, inda ya ce ya
kamata Majalisar Tarayya ta kafa wata doka da za ta hana
mabarata yawo a kasar nan.


A cewarsa, “ya kamata dokar ta tilasta wa iyaye da wadanda
nauyin kula da ’ya’ya rataya a wuyansu su rika sanya ’ya’yansu
a makaranta.”


Ya kara da cewa, “matsalar tsaro da ayyukan ta’addanci da ake
fuskanta a kasar nan na da nasaba ne da rashin neman ilimi
musamman a yankin Arewa maso Gabas da wasu jihohi.