Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, ta ce ta harba makaman roka cikin arewacin Isra’ila, a matsayin martani kan harin Isra’ilar na ranar Asabar.
Ƙungiyar da ke samun goyan-baya daga Iran ta ce makamanta sun fada a garin Kiryat Shmona da ke Isra’ila.
To amma jami’ai a yankin na cewa makaman roka biyar aka harba, sai dai babu wanda aka bayar da rahotan jikkata ko rasa rayuka.
Kafin wannan lokaci, ma’aikatar lafiyar Lebanon ta bayar da rahoton cewa an kashe jami’an agajin gaggawa uku da kuma jikkata wasu biyu a harin da Isra’ila ta kai musu da jirage marasa matuƙa.
The ministry said the crew had been putting out fires caused by earlier Israeli strikes in a village in southern Lebanon.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa ma’aikatan agajin na ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi sakamakon hare-haren Isra’ila a wani ƙauye da ke kudancin Lebanon.