Wata gagarumar zanga-zanga ta ɓarke a biranen Isra’ila, don neman gwamnatin ta dawo da ‘yan ƙasar da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
Masu shirya zanga-zangar sun ce kusan mutum 500,000 ne suka fantsama kan tittuna a Tel Aviv, tare da yi wa ginin ma’aikatar tsaron ƙasar ƙawanya.
Sannan ana gudanar da makamaciyar wannan zanga-zanga akai- akai a biranen Kudus da Haifa.
Daya daga cikin masu zanga-zangar ta ce sun gaji da jira kimanin wata 11 da ake garkuwa da mutanen, waɗanda wasu daga cikinsu suka riga suka mutu.
Kusan a kullum ake irin wannan gangamin tun bayan gano gawarwakin ‘yan Isra’ila shida a Gaza kwanaki takwas da suka gabata.
Masu boren na son Firaminita Netanyahu, ya amince da cimma yarjajaniyar da za ta bayar da damar sako sauran mutanen da ake garkuwa da su.