Akalla mutane 21 suka rasa rayukansu a hare-haren sama da aka
kaddamar cikin dandazon mutane da ke cin kasuwa a yankunan
kudu maso gabashin Sudan.
Kungiyar liktoci ta Sudan ta ce dakarun RSF ne suka kai harin a birnin Sennar.
Sannan Akwai gwamman mutanen da aka jikkata. Wannan rikici tsakanin sojoji da rundunar mayakan RSF ya tilastawa fararan-
hula da dama tserewa daga yankunan Jihar Sennar baya ga wadanda yaƙin ke kashewa.