Home Labaru Hawan Daushe A Kano: Shugaban Kasar Guenea Ya Halarci Taron

Hawan Daushe A Kano: Shugaban Kasar Guenea Ya Halarci Taron

400
0

Masarautar Kano a Najeriya ta shirya kasaitaccen Hawan Daushe tare da halartar shugaban kasar Guinee Conakry Alpha Conde.

Alpha Conde, Wanda ya gudanar da sallar idi a garin Daura na jihar Katsina, a marecen jiya ya halarci bikin hawan sallar da aka yi a fadar mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi na biyu a Kofar Kudu.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya halartarci bukin karon farko tun bayan takaddama da suka samu da sarki Sunusi na biyu.

A bangare daya jami’an tsaro sun tarwatsa wasu gungun masu adawa da karin sabbin masarautu da gwamnatin jihar ta yi.

Kafin tarwatsa su, suna rera wakokin da ke cewa “sarki daya ne a Kano”.