Home Labaru Hong Kong: An Sake Bude Filin Jiragen Sama Bayan Zanga-Zanga

Hong Kong: An Sake Bude Filin Jiragen Sama Bayan Zanga-Zanga

221
0

An sake bude filin sauka da tashin jiragen saman Hong Kong, bayan da dubban masu zanga-zanga suka mamaye filin jiragen sama.

Shugabar gwamnatin yankin na Hong Kong Carrie Lam ta yi gargadin cewa ci gaba da wannan tarzomar lamari ne da zai jefa yankin a cikin hali na rashin tabbas.

Carrie Lam

Bayan share tsawon makonni 10 suna gudanar da tarzomar nuna kin jinin gwamnatin Carrie Lam, a ranar litinin dubban masu rajin kare dimokuradiyyar suka mamaye filin jiragein saman Hong Kong, daya daga cikin filayen jiragen sama mafi hada-hada a duniya.

Tarzomar ta yi sanadiyyar dakatar da sauka da tashin daruruwan jirage a tsawon yinin na Litinin, lamarin da ya kara jefa kasuwar hannayen jari da sauran harkokin tattalin arziki cikin hali na rashin tabbas a yankin.

Mahukuntan China, kasar da ta karbi ragamar tafiyar da wannan yanki mai kwarya-kwaryan ‘yancin cin gashin kai daga hannun Birtaniya a 1997, sun fusata sakamakon kutse a filin jiragen saman, tare da bayyana wasu daga cikin masu zanga-zangar a matsayin ‘yan ta’adda

To sai dai duk da cewa an fara jigilar fasinja Talalatan nan, wasu daga cikin masu fafutukar sun bukaci a gudanar da wata zanga-zanga da marece  don mamaye filin jiragen saman.