Home Labaru Goron Sallah’: Tambuwal Ya Rabawa Alhazan Sokoto Naira Miliyan 70

Goron Sallah’: Tambuwal Ya Rabawa Alhazan Sokoto Naira Miliyan 70

266
0

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya raba naira miliyan 70 ga alhazan jihar da a yanzu haka ke kasar Saudiyya suna gabatar da ibadun aikin Hajji.

Kakakin mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdullahi Abubakar ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar, inda ya mika gaisuwar sallah ga alhazan Sakkwato ya yin da suke garin Muna a kasar Saudiyya.

Ya ce gwamna Aminu Tambuwal, ya amince da biyan kowanne Alhaji da Hajiya Riyal dari 200, kwatankwacin naira dubu 24 ga dukkanin alhazan jihar s dubu 3 da dari  496 a matsayin Barka da Sallah.

Gwamnan, ya yi haka ne, domin tallafawa alhazai dake neman taimako bayan guzurinsu ya fara yin kasa domin su sami kudin cin abinci da kuma zirga-zirga.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya nemi mahajjatan su jajirce wajen yi wa jihar Sakkwato addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai daurewa, da ma Najeriya gaba daya.