Wani jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji ya murƙushe tirela ɗauke da siminti da babur ɗin Adaidaita Sahu a Kano.
Lamarin ya faru ne a kan titin Obasanjo a safiyar Lahadi, inda waɗanda suke kasuwancin a kusa da layin dogon sun bayyana cewa sun hango tirelar tana zuwa a lokacin da jirgin ƙasan ya taho da gudu
Sun bayyana cewa sun yi ƙoƙarin jan hankalin direban tirelan amma bai ankara ba.
Babu tabbaci kan ko wani ya mutu a hatsarin amma an bayyana cewa an kai waɗanda suka samu rauni asibitin Murtala da ke Kano.