Home Home Wata Sabuwa: Babu Ni Babu Goyon Bayan Wata Jam’iyyar Siyasa – Obasanjo

Wata Sabuwa: Babu Ni Babu Goyon Bayan Wata Jam’iyyar Siyasa – Obasanjo

70
0

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya jaddada matsayarsa ta rashin goyon bayan ko wacce irin jam’iyyar siyasa, yana cewa shi yanzu babu abin da zai sa ya shiga wata siyasar jam’iyya.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kammala tattaunawa da shugabannin majalisar kolin jam’iyyar PDP a Abeokuta.

Obasanjo ya ce ya gwammace ya zama dattijo a gefe guda, yana cewa ba shi babu siyasar da ke cikin jam”iyyu.

 Ya ce Ina son kara jaddada matsayata cewa ba ni da wata jam’iyyar siyasa yanzu, babu kuma abin da zai sa na yi.

A ko da yaushe na fi son Najeriya ta ci gaba, kuma ina tare da duk wanda yake shirye ya dauki shawarata, ko da yaushe zan so ganin abin da zaikawo wa Najeriya da Afrika ci gaba.

Obasanjo, ya ce shi ne dalilin da kaga hakkin da yake wuyana na abin da yake faruwa a gabashin Afrika, wanda kuma sulhu kan haka ba abu bane mai sauki.