Home Home Hana Fasakwaurin Kayan Tarihi: Najeriya Da Amurka Sun Kulla Yarjejeniya

Hana Fasakwaurin Kayan Tarihi: Najeriya Da Amurka Sun Kulla Yarjejeniya

80
0
Najeriya da Amurka sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da za ta kare kayayyakin al'adu da tarihi ta hanyar hana fasaƙwaurin su.

Najeriya da Amurka sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da za ta kare kayayyakin al’adu da tarihi ta hanyar hana fasaƙwaurin su.

Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard da Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu na Najeriya Lai Mohammed ne suka sa hannun kan yarjejeniya a nan Abuja.

Yarjejeniyar ta tanadi cewa Amurka za ta ƙwace duk wasu kayan tarihi da aka yi fasaƙwaurin su zuwa ƙasar daga Najeriya nan take sannan ta mayar da su ba tare da an bi ta hanyar kotu ba ko kuma wasu hanyoyin difilomasiyya.

Lai Mohammed, ya ce ƙulla yarjejeniyar ya zama dole saboda duk yunƙurin Ma’aikatar Yaɗa Labarai na daƙile fasa-ƙwaurin kayan tarihi na Najeriya zuwa ƙasashen waje har yanzu lamarin na ci gaba.

Ya ƙara da cewa akasari ana kai kayan tarihin ne zuwa Turai da Amurka da sauran wurare da zimmar amfanar masu tattara kayan tarihi.

Ita ma Jakadiya Mary Beth ta ce yarjejniyar ta duba abin da ya faru a baya da kuma alkintawa tare da dawo da kayan tarihi na gado a Najeriya.