Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Hatsari: Jirigin Ƙasa Ya Yi Karo Da Tirela Da Adaidaita Sahu A Kano

Wani jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji ya murƙushe tirela ɗauke da siminti da babur ɗin Adaidaita Sahu a Kano.

Lamarin ya faru ne a kan titin Obasanjo a safiyar Lahadi, inda waɗanda suke kasuwancin a kusa da layin dogon sun bayyana cewa sun hango tirelar tana zuwa a lokacin da jirgin ƙasan ya taho da gudu

Sun bayyana cewa sun yi ƙoƙarin jan hankalin direban tirelan amma bai ankara ba.

Babu tabbaci kan ko wani ya mutu a hatsarin amma an bayyana cewa an kai waɗanda suka samu rauni asibitin Murtala da ke Kano.

Exit mobile version