Home Labaru Hasashe: Za A Sami Ambaliya A Legas Da Jihohin Kewaye- NEMA

Hasashe: Za A Sami Ambaliya A Legas Da Jihohin Kewaye- NEMA

519
0

Hukumar bayar da agajin gaugawa ta Najeriya NEMA, ta yi gargadi cewa za a ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa a jihohin Legas da kewayen ta.

Mai magana da yawun Hukumar Ibrahim Farinloye

Mai magana da yawun Hukumar Ibrahim Farinloye, ya bayanna haka , inda ya ce jama’a su sa ran cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya  a watan Satumba mi zuwa.

Farinloye, ya bayyana hakan ne  a lokacin da yake magana a wajen wani taron da hukumar  shirya, ya ce  binciken da su ka yi ya nuna cewar za a yi ambaliya a jihar Legas da jihohin dake akwabtaka da ita a wannan shekarar .

Ya ce za a sami matsalar ne saboda rashin hanyoyin ruwa a cikin birane da kauyuka a  jihohin kudu maso yammacin Najeriya, saboda haka hukumar ta sanar da gwamnonin yankin.

Hukumra ta NEMA ta daura laifin ne kan jihohi da kananan hukumomi wadanda  ba sa gina hanyoyin  ruwa, inda hukumar ta bayar da kwatance da jihar  Legas, akan yadda aka cika hanyoyin ruwa da bola da tarkace.