Home Labaru Gobarar Legas: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Fara Gudanar Da Bincike

Gobarar Legas: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Fara Gudanar Da Bincike

337
0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Legas ta ce za ta fara gudanar da bincike akan abinda ya janyo wata gobara da ta kashe mutane  Unguwa takwa-Bay da ke jihar.

Gobara ta yi sanadiyyar mutuwar wasu yara ‘yan gida daya su biyar, inda yanzun haka aka fara bincike a game da wannan hadari.

Jami’an ‘yan sandan daken a jihar sun fara tattara hujjoji da bayanai game da wannan gobara domin bada cikakken rahoto.

Bala Elkana, Kakakin ‘yan sanda na jihar Legas

Kakakin ‘yan sanda na jihar Legas, Bala Elkana, ya tabbatarwa jama’a aukuwar wannan gobara, inda ya ce wannan annoba ta gobara ta kashe wasu yara ‘yan gida daya, kuma rundunar na bincike halin yanzun.