Home Labaru Haramta Shi’a: Manyan Lauyoyin Najeriya 2 Sunyi Karin Haske

Haramta Shi’a: Manyan Lauyoyin Najeriya 2 Sunyi Karin Haske

378
0

Wasu manyan lauyoyin Najeriya biyu da suka hada da Mike Ozekhome da Femi Falana sun ce haramta ayyukan kungiyar Shi’a da gwamnatin tarayya ta yi ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Lauyoyin sun ce babban laifi ne  umurnin da gwamnatin tarayya ta karbo daga babban kotun tarayya ta Abuja na haramta ayyukan kungiyar.

Mike Ozekhome da Femi Falana

Ozekhome,  ya ce sashi na 10 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce Najeriya, kasa ba ce da ke yin hukunci ko doka da wani addini saboda haka gwamnati ba za ta iya haramta wani addini ba.

Ya ce Shi’a kungiyar addini ce ba kungiya bace da za a iya haramtawa,  saboda haka ba za ka iya haramta addini ba, abinda mutane su ka yi imani da shi.

Shi ma Femi Falana ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta janye haramcin da ta kakaba kan kungiyar, domin ba dai-dai bane wadanda ke mulki su yi amfani da dokar kasa domin ruguza wata kungiya wanda wadanda ke yin ta na ganin addini ce.

Falana,  ya ce  ya kamata a janye haramta kungiyar Shi’a da a ka yi domin ya ci karo da hakkin dan kasa na yin addini da kundin tsarin mulki ya ba kowa.