Home Labaru An Kara Wa Sojin Da Ya Maida Naira Miliyan 15 Da Ya...

An Kara Wa Sojin Da Ya Maida Naira Miliyan 15 Da Ya Tsinta Girma

461
0

Rundunar sojin sama ta Nijeriya, ta yi wa jami’in da ya maida naira miliyan 15 da ya tsinta karin girma har mataki biyu.

Jami’in mai suna Bashir Umar, ya na daga cikin Tawagar Kar-ta-Kawana ta Mayakan Sama da aka tura filin jirgin sama na Kano domin tabbatar da tsaro.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin saman ta ce Bashir ya na tare da wani abokin aikin sa suna sintiri, yayin da ya tsinci damin kudin, amma maimakon ya danne sai ya duba jikin takardar da kudin ke nade ya ga lambar wayar mai su ya kuma kira shi.

An dai kara wa jami’in girma ne daga mukamin kurtu zuwa kofur, yayin da Babban hafsan sojin sama na Nijeriya Air Marshal Sadique Abubakar, ya bayyana Umar a matsayin mai kyakkyawan hali abin koyi ga sauran jami’ai.

Umar, wanda ya halarci taron girmama shi tare da iyayen sa, ya ce ya maida kudin ne ga mai su saboda tasirin dabi’un gidan su da na aikin sa.