Home Labaru Martani: Ban Ce Ba Na Son Mukamin Minista Ba- Audu Ogbeh

Martani: Ban Ce Ba Na Son Mukamin Minista Ba- Audu Ogbeh

275
0

Tsohon ministan ayyukan gona da raya karkara, Audu Ogbeh ya musanta rahotannin da suke karade wasu kafafen yada labarai na zamani cewar an yi masa tayin minista amma ya ce baya so.

Audu Ogbeh, ya bayyana hakan ne yayin da wata tawagar kungiyar  ci gaban kabilar Idoma a karkashin jagorancin Jacob Okwori,  suka ziyarce shi a Abuja, domin samun karin bayyani kan dalilin da yasa ba a sake nada shi minista ba.

Ya ce bai taba cewa baya  son shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada shi a  matsayin minister, saboda babu wanda ya tuntube shi a madadin shugaban kasa tun bayan da suka ajiye aiki a ranar 29 ga watan Mayu.

Ya ce karya ce kawai tsantsagawaron ta kuma sharri ne aka yi cewa wai ya ce baya son a sake nadashi minister, amma ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bi sa bashi damar yi wa Najeriya hidima.