Home Labaru Hana Safarar Kwayoyi: Buhari Ya Umurci Ndlea Ta Dauki Ma’aikata 5,000

Hana Safarar Kwayoyi: Buhari Ya Umurci Ndlea Ta Dauki Ma’aikata 5,000

413
0

Shugaban hukumar NDLEA, Kanal Muhammad Abdallah, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince da bukatar hukumar na daukar ma’aikata 5,000 don karfafa ayyukan rundunar a damarar da ta sha na yaki da safara da kuma shan miyagun kwayoyi a Najeriya.

Shugaban hukumar NDLEA, Kanal Muhammad Abdallah

Abdallah, ya bayyana haka ne yayin gangamin lalata wasu miyagun kwayoyi da reshen hukumar ta jihar Traraba tayi a garin Jalingo.

Ya kuma kara da cewa, daukar ma’aikatan zai taimaka kwarai da gaske wajen kokarin da gwamnati ke yi na yaki da shan miyagin kwayoyi da kuma safarar su, abin da ya addabi al’umma musamman a tsakanin matasan Nijeriya.

Ya kara da cewa, yadda matasa ke kwankwadar miyagun kwayoyi a jihar Taraba na da tayar da hankali, dan haka ya kamata iyaye su kawo nasu daukin don ganin an kawo karshen wannnan tashin hankalin.