Home Labaru Sakin Zakzaki: Fadar Shugaban Kasa Tace Buhari Bashi Da Iko

Sakin Zakzaki: Fadar Shugaban Kasa Tace Buhari Bashi Da Iko

179
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Fadar shugaban kasa ta ce bada umurnin ci gaba da tsare shugaban mabiya addinin shi’a Ibrahim Zakzaky abu ne na bangaren shari’a ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimakawa shugaban kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu.

Garba Shehu, mai taimakawa shugaban kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a

Ta bukaci ‘yan shi’a dake zanga-zanga a Abuja da wasu sassan Najeriya da su daina su kuma jira hukuncin da kotu za ta yanke.

Fadar shugaban kasar ta ce komai tsananin zanga-zanga da mabiya addinin shi’a ke yi ba zai sa shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa bangaren harkokin shari’a katsalandan ba.

Sanarwar ta kara da cewa yanzu haka shari’ar na gaban kotu a Kaduna, domin haka duk mutumin da aka samu da saba doka da lalata kayayyakin gwamnati zai fuskanci fushin hukuma.

Fadar shugaban kasar ta kuma gargadi mabiya shi’an da su guji tauye hakkin sauran ‘yan kasa da sanya fargaba a zukatan su, domin hakan ya sabawa dokar kasa. z