Home Labaru Aikin Hajji: NAHCON Ta Shawarci Mahajjata

Aikin Hajji: NAHCON Ta Shawarci Mahajjata

200
0
NAHCON, hukumar alhazai ta kasa

Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta shawarci maniyyatan Najeriya da su kasance masu tsam cikin natsuwa kan abubuwan da suka shafi tsaro a kasa mai tsarki.

Shugaban sashen wayar da kan mahajjata da maniyyata na kungiyar Umar Bala, ya bada shawarar a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan zantawa da mahajjatan jihohin Kano, Kwara, Osun da Katsina a birnin Madina.

Umar Bala, Shugaban sashen wayar da kan mahajjata da maniyyata na kungiyar.

Ya ce burin hukumar shine kowanni maniyyaci ya samu aikin hajji karbabbe.

Sannan ya bukaci wadanda suka je aikin Hajjin da su tuntubi jami’an hukumar kan duk wani abu da ya shige musu dan gudun fadawa hannun muggan mutane da za su cutar dasu.

Ya kuma yabawa mahajjatan kan irin dabi’u na gari da suka nuna, tare da cewa hukumar za ta ci gaba da wayar da kansu musamman kan yadda za su kula da kayayyakin otel-otel din da aka sauke su. ⚛3�$�