Wakilan gwamnatin tarayya sun gana da shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya, a kan aiwatar da sabon tsarin mafi karancin albashin Naira 30,000 da kuma yin gyara a albashin ma’aikatan gwamnati.
An dai fara ganawar ne, jim kadan bayan isowar ‘yankungiyar a ma’aikatar kwadago da daukar ma’aikata a Abuja da ke Abuja.
Da ya ke jawabin sa, ministan kwadago Chris Ngige, ya ba shugabannin kungiyar tabbacin cewa zai cigaba da kasancewa a tsaka-tsaki a tattaunawar, tsare da yaba wa ‘yan kungiyar bisa nuna fahimta da su ka yi.
Ngige ya sanar da cewa, za a sake wani zama tare da shugabannin hukumomin gwamnati, domin tattaunawa a kan albashin da za a iya biyan ma’aikata.
Da
farkon zaman an hana ‘yan jarida daukar rahoton ganawar da aka yi cikin sirri,
amma daga bisani sai ministan ya ba su damar shiga.














































