Home Labaru Kotun ECOWAS Ta Bukaci Nijeriya Ta Biya Wani Soja Diyyar Naira Miliyan...

Kotun ECOWAS Ta Bukaci Nijeriya Ta Biya Wani Soja Diyyar Naira Miliyan 10

224
0

Kotun habbaka tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS, ta umarci Gwamnatin Nijeriya ta biya wani soja Barnabas Eli diyyar naira milyan 10.

Umarnin dai ya biyo bayan korar shi da aka yi ne saboda bindigar da aka damka ma shi ya na aiki da ita ta bace a hannun sa cikin shekara ta 2012.

Haka kuma, kotun ta umarci a biya shi dukkan albashin sa da sauran hakkokin sa, tun daga watan Maris na shekara ta 2015 zuwa ranar da aka sake shi daga tsarewar da aka yi ma shi.

Bacewar bindiga a hannun Eli ta janyo masa daurin shekaru biyu a kurkuku, ba tare da sanar da hukuma cewa an yanke ma shi hukuncin dokar soja ba.

Da ta ke yanke huncin, Kotun ECOWAS ta yi amfani da Doka ta 90 (40), inda ta ce an tauye wa sojan ‘yancin sauraren ba’asin sa a cikin lokaci. Sojan dai ya kai kara ne cikin shekara ta 2016, inda ya zayyana cewa a cikin shekara ta 2012, ya na aiki a matsayin sa Sojan Nijeriya, sai aka sace bindigar sa a Riyom na jihar Jihar Filato.