Home Labaru Kiwon Lafiya: Akwai Yiwuwar Barkewar Cutar Tetanus A Jihohi 11 Na Arewacin...

Kiwon Lafiya: Akwai Yiwuwar Barkewar Cutar Tetanus A Jihohi 11 Na Arewacin Nijeriya – UN

239
0

Majalisar dinkin duniya, ta ce akwai yiwuwar barkewar cutar Tetanus a jihohi 11 da ke arewacin Nijeriya, kamar yadda jami’in ta Dakta Idris Nagya ya bayyana a wajen wani taron wayar da kai da ya gudana a birnin Minna na jihar Neja.

Ya ce yiwuwar barkewar annobar ta shafi kananan hukumoi 138, tare da jaddada cewa, za a fi samun masu cutar a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Ya ce kananan hukumomin jihar Neja da ke fuskantar yiwuwar barkewar cutar, sun hada da Agwara da Edati da Magama da Mashegu da Mokwa da Rafi da kuma Shiroro.

Nagya, ya kuma danganta lamarin da yawaitar rashin ilimi da al’adu da addini da kuma rashin isassun cibiyoyin kiwon lafiya da ya kamata masu ruwa da tsaki su shawo kai.

Daraktar rigakafin cibiyoyin lafiya na jihar Neja Dakta Fati Sheik Abdullah, ta ce akwai yiwuwar wayar da kan da ake yi a kan cutar ta Nijeriya ta yi amfani, sakamakon kokarin da kafafen yada labarai ke yi.