Home Home Gwamnatin Najeriya Za Ta Samar Da Jami’an Tsaro Don Kare Tasoshin Jiragen...

Gwamnatin Najeriya Za Ta Samar Da Jami’an Tsaro Don Kare Tasoshin Jiragen Ƙasa

139
0
Gwamnatin tarayya ta ce za ta samar da jami’an tsaro na musamman, wadanda za su riƙa kula da sufurin jiragen ƙasa a wani ɓangare na matakan magance hare-haren da ake kai wa jiragen da fasinjoji.

Gwamnatin tarayya ta ce za ta samar da jami’an tsaro na musamman, wadanda za su riƙa kula da sufurin jiragen ƙasa a wani ɓangare na matakan magance hare-haren da ake kai wa jiragen da fasinjoji.

Ƙaramin ministan sufuri Ademola Adegoroye ya bayyana haka, lokacin da ya kai ziyara tashar jirgin ƙasa ta Tom Ikimi a  ƙaramar hukumar Igueben ta jihar Edo.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya za ta ɗauki matakan da su ka dace domin magance matsalar hare-hare a kan tasoshin jiragen ƙasa, domin tabbatar da kariya ga fasinjoji da kayayyakin aikin hukumar.

Daga cikin matakan da ya ce hukumar za ta ɗauka, akwai haɗa kai tsakanin hukumar da al’umma mazauna yankunan da tasoshin jiragen su ke, domin samar da tsaro ga tasoshin jiragen.

Ministan, ya kuma yi watsi da fargabar da ake yi cewa gwamnati za ta rufe zirga-zirgar jiragen ƙasa a faɗin Nijeriya, ya na mai cewa gwamnatin tarayya da hukumar sufurin jiragen ƙasa ba su da wannan niyya.

Leave a Reply