Home Home Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar Da NNPP Ta Shigar Da Uba...

Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar Da NNPP Ta Shigar Da Uba Sani

33
0
Kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna, ta yi fatali da karar da jam’iyar NNPP ta shigar, ta na kalubalantar hukumar zabe da Jam’iyar APC da dan takarar ta na gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani.

Kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna, ta yi fatali da karar da jam’iyar NNPP ta shigar, ta na kalubalantar hukumar zabe da Jam’iyar APC da dan takarar ta na gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani.

Lauyan jam’iyyar APC kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Kaduna, Sule Shu’aibu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce karar jam’iyyar NNPP ta daukaka a Kaduna bisa tuhumar hukumar zabe da APC, tare da neman a soke tikitin dan takarar gwamnan jam’iyyar APC da ‘yan majalisun jiha 34 an yi watsi da ita.

A baya dai Kotu ta yanke hukuncin cewa, jam’iyyar NNPP ta makara wajen shigar da karar domin lokaci ya wuce, amma sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin Hunkuyi da jam’iyar NNPP su ka zarce zuwa Kotun daukaka kara.

Masu karar sun yi zargin cewa, jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin taro na zaben wadanda ke da alhakin kaɗa kuri’a domin fitar da dan takarar gwamna da na majalisar dokoki ta jiha ba.