
Gwamnatin jihar Rivers, ta shigar da sabuwar kara a kan tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, bisa zargin yin sama da fadi da Naira biliyan 96.
An dai maka Rotimi Amaechi tare da dan takarar gwamnan Jam’iyyar APC na jihar Tonye Cole bisa zargin saida kadarorin jihar Rivers.
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya kafa wani kwamitin mutane bakwai domin binciken Amaechi a kan zargin cirar Naira biliyan 96 daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da ya ke gwamna.
Kwamitin, ya kuma binciki batutuwan da su ka shafi saida kadarorin da tsohon gwamnan ya yi, bayan ya ya gabatar da rahoton sa a shekara ta 2015, amma Amaechi ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa.
A ranar 27 ga watan Mayu na shekara ta 2022 ne, wata babbar kotu ta yi watsi da bukatar Amaechi na hana kwamitin gudanar da bincike a kan sa.
You must log in to post a comment.