Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya bukaci bangaren zartarwa ya tabbatar an gabatar da kasafin shekara ta 2020 a majalisar dokoki ta tarayya nan da watan Satumba na shekara ta 2019.
Gbajabiamila ya bayyana bukatar ne, yayin wata ganawa da sakataren gwamnatin tarayya a majalisar dokoki ta kasa da ke Abuja. Ya ce gabatar da kasafin da wuri zai tabbatar da ganin majalisa ta tantance shi cikin watanni uku, wanda ta haka ne za a maida Nijeriya a kan tsarin kasafi na Janairu zuwa Disamba.