Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ta bada umarnin kwace wasu makudaden kudade na uwargidan tsohon shugaban kasa Patience Jonathan domin mallaka wa gwamnatin tarayya.
Kudaden da kotun ta kwace dai, sun hada da Naira miliyan 9 da dubu 200, da kuma Dala miliyan 8 da miliyan 4 da ke bankunan Diamond da Fidelity da Eco da Stanbic da Skye da Zenith da kuma First Bank.
Yayin yanke hukuncin, Mai shari’a Olatoregun ta ce, babu gamsassun hujjojin da za su hana ayyana kudaden a matsayin wandanda aka same su ba ta haramtattun hanyoyi ba.
A baya dai Hukumar EFCC ta samu izinin wucin-gadi na karbe kudaden, yayin da a wannan karon kotu ta bada izinin karbewa na din-din-din. Sai dai a kokarin kare kan ta, Patience Jonathan ta bayyana wa kotun cewa, ta samu kudaden ne daga gudunmuwar da wasu mutanen kirki ‘yan Nijeriya su ka ba gidauniyar ta a lokacin da Jonathan ke kan kujerar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, da zuwa lokacin da ya zama shugaban kasa.