Home Labaru Ba Zan Ba Ku Kunya Ba – Buhari

Ba Zan Ba Ku Kunya Ba – Buhari

885
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce sakamakon zaben shekara ta 2019 ya nuna zabin ‘yan Nijeriya ne, don haka ba zai ba al’ummomin shi kunya ba tun da su ka sake zaben sa a karo na biyu.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin kungiyar masu goyon bayan sa a karkashin jagorancin da shugaban ta Alhaji Umaru Dembo a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Buhari, ya ce gwamnatin sa za ta yi wa ‘yan Nijeriya aiki tukuru a kan gaskiya, musamman wajen zakulo albarkatu da nada mutanen da za su kawo wa kasa ci-gaba.

Ya ce zaben shekara ta 2019 ya wuce, kuma ‘yan Nijeriya sun sun yi magana da babbar murya ta hanyar sake zaben shi, don haka yanzu lokaci ne na yi masu aiki tukuru. Shugaban Buhari,  ya kuma mika sakon godiya ta musamman ga kungiyar bisa tsayawa tare da shi a duk gwagwarmayar sa ta siyasa tun daga shekara ta 2002.