Home Labaru Gbajabiamila Ya Nemi A Mika Kasafin 2020 A Satumba

Gbajabiamila Ya Nemi A Mika Kasafin 2020 A Satumba

331
0
Femi Gbajabiamila, Shugaban Majalisar Wakilai

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya bukaci bangaren zartarwa ya tabbatar an gabatar da kasafin shekara ta 2020 a majalisar dokoki ta tarayya nan da watan Satumba na shekara ta 2019.

Gbajabiamila ya bayyana bukatar ne, yayin wata ganawa da sakataren gwamnatin tarayya a majalisar dokoki ta kasa da ke Abuja. Ya ce gabatar da kasafin da wuri zai tabbatar da ganin majalisa  ta tantance shi cikin watanni uku, wanda ta haka ne za a maida Nijeriya a kan tsarin kasafi na Janairu zuwa Disamba.

Leave a Reply