Home Labaru Ganduje Ya Ce ‘Yan Bindiga Sun Kwace Dajin Falgore

Ganduje Ya Ce ‘Yan Bindiga Sun Kwace Dajin Falgore

109
0

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya koka kan yadda ‘yan bindiga suka mamaye dajin Falgore.

Gwamnan wanda ya zanta da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, ya bukaci gwamnatin tarayya ta kawo agaji ga jihar Kano da wasu jihohi uku da suka raba dajin.

Gnaduje, ya bayyana kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasar a matsayin abin takaici.