Home Labaru Gwamnonin APC Sun Ce Ganduje Tauraro Ne A Siyasar Najeriya

Gwamnonin APC Sun Ce Ganduje Tauraro Ne A Siyasar Najeriya

358
0

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC (PGF) ta bayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano a matsayin tauraro mai haske a siyasar Najeriya.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar taya murnar da ta yi wa Ganduje yayin da ya cika shekaru 72 a duniya.

Gwamnan Jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar PGF, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai ranar Asabar a nan Abuja.

Da yake jawabi, gwamna Bagudu ya ce Ganduje jagora ne na gari kuma mai hangen ne sa da ya jajirce don tabbatar da hadin kan al’umma da kuma samar da Najeriya dunkulalliya.

Kazalika, Shugaban na kungiyar PGF ya bayyana gwamna Ganduje a matsayin jagora na hakika, la’akari da ayyukan da ya aiwatar domin ci gaban jam’iyyar APC.

Ya jaddada kudirin kungiyar wajen ganin ta aiwatar da shirye-shiryen da ta sanya a gaba na bunkasa jihohin su ta hanyar samar da ayyukan yi, bunkasa tattalin arziki, dakile rashin daidaito da kuma rage talauci.

Leave a Reply