Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Labarin Shirin Kai Hari A Abuja

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Labarin Shirin Kai Hari A Abuja

61
0

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya Ra’uf Aregbesola ya karyata rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai dangane da cewa bakin ‘yan ta’adda daga kasashen waje na barazanar kai hare-haren ta’addanci a nan Abuja.

Aregbesola, ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai kan sakamakon taron gaggawa na majalisar tsaron Najeriya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewar Ministan, Abuja na cikin kwanciyar hankali da samun cikakken tsaro daga dukkanin wata barazana ta fuskantar hare-haren ta’addanci.

Ministan cikin gidan ya kara da cewar, ba aibu bane a samu bullar wani rahoto da ke jan hankalin hukumomin tsaron Najeriya dangane da wata barazana komai kankantar ta, dan haka sanarwar da ta bulla a kwanakin baya kan yiwuwar fuskantar harin ‘yan ta’adda daga kasar Mali, bayanai ne da aka saba musayar su yayin tafiyar da aiki a tsakanin hukumomin tsaro, wadanda mutane ba sa bukatar su tayar da hankalin su akai.