Rundunar sojin Ukraine ta ce wani harin sama da Rasha ta kai da daddare kan babban birnin ƙasar, Kyiv, ya lalata gine-gine da tituna da layukan lantarki.
Sojojin sun kuma ce wasu rahotanni da aka bayar tun da farko na wata wuta da ta tashi ba su illata kowa ba.
Ana ta ankarar da jama’a a yawancin sassan gabashin ƙasar ta Ukraine saboda hare-haren da Rasha ke kaiwa tun daren Asabar.
Shugaba Zelensky ya faɗa a shafukan sada zumunta da muhawara cewa sannu a hankali yanzu Rasha na amfani da jirage marassa matuƙa ƙirar Iran, samfurin Shahed da kuma makamai masu linzami.
Ma’aikatar tsaro ta Rasha ta ce garkuwarta ta sama ta yi nasarar tare hare-haren jirage marassa matuƙa har goma sha tara a cikin dare, waɗanda ta hari kudu maso yammacin ƙasar