Ofishin Majalisar Dinkin Duniya, mai lura da al’amuran jin ƙai ya yi hasashen samun matsananciyar yunwa a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka.
Cikin wani saƙo da ofishin ya wallafa a shafinsa na X, ya yi gargaɗin samun tsanantar matsalar a Najeriya tsakanin watan Nuwamban 2024 zuwa watan Mayun 2025.
Ya ce ya kamata a ɗauki matakai domin yaƙi da yunwa da ceto rayukan mutane a yanzu da kuma tsawon lokaci a nan gaba kamar yadda ofishin ya wallafa.
Bayanan da ofishin ya fitar sun nuna cewa a Najeriya, mutum miliyan 38 ne za su fuskanci matsalar.
yayin da ƙasar Sudan ta Kudu ke biye mata da mutum miliyan 21, sai ƙasar Ethiopia mai mutum miliyan 15.
A farkon wannan shekarar ne dai gwamnatin tarayya ta sanar da wasu matakai uku na kawo sauƙi ga matsalar ƙarancin abinci a ƙasar.
Ɗaya daga cikin matakan shi ne, gwamnatin ta fito da tan 42,000 na abinci daga rumbunan ma’aikatar harkokin noma da nufin kawo sauƙi ga al’ummar ƙasar.