Jam’iyyar Labour da ke mulkin jihar Abia ta kasa cin ko da ɗaya daga ƙananan hukumomin jihar 17 a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jiya Asabar.
A maimakon haka jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP), ce ta cinye yawancin ƙananan hukumomin inda ta samu 15 daga cikin 17.
Jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) ce ta ci ragowar ƙananan hukumomin biyu – ƙaramar hukumar Ugwunagbo da kuma Osisioma Ngwa.
Shugaban hukumar zaɓen jihar, (ABSIEC), George Chima, shi ne ya bayyana sakamakon a ofishin hukumar da ke babban birnin jihar, Umuahia, a jiya Asabar.
Mista Chima, ya bayyana gamsuwarsa da yadda zaɓen da ya ce sama da jam’iyyu 12 suka shiga, ya gudana.
Sakamakon rigimar da ake yi ta shugabancin jam’iyyar Labour a tarayya, ‘yan takarar da ake gani suna da goyon bayan gwamnan jihar Alex Otti, sun tsaya takara ne a jam’iyyar Zenith Labour Party, wadda ta ci kujeru 15 ɗin