Home Labarai Uwargidan Shugaba Tinubu Sa Ribadu Za Su Jagoranci Yi Wa Kasa Addu’a

Uwargidan Shugaba Tinubu Sa Ribadu Za Su Jagoranci Yi Wa Kasa Addu’a

40
0
59355376
59355376

Uwargidan shugaban ƙasa, Da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Ribadu za su jagoranci addu’a ta musamman domin neman sauƙin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Za a gudanar da addu’ar ne ƙarƙashin jagorancin jagororin addinin Musulunci da Kirista, domin neman taimakon Allah a kan ƙalubalen da suka yi ƙasar dabaibayi.

Chief Segun Balogun Afolorunikan, wanda shi ne darakta-janar na shirya addu’ar ta ƙasa ne ya sanar da hakan a Abuja,

Ya ce akwai buƙatar kowa ya bayar da nasa gudunmuwar domin magance matsalar da ƙasar ke fuskanta.

inda ya nanata cewa haɗin kai na da muhimmanci wajen shawo kan dukkan matsala.

Ya kara da cewa Bayan addu’ar suna da yaƙinin Allah zai buɗe mana hanyoyin da za mu samu sauƙi,” Afolorunikan.

inda ya ƙara da cewa Najeriya za ta shiga shekarar 2025 cikin walwala.

Leave a Reply