Home Labaru Fashola Ya Ce Ma’aikatar Sa Ta Dawo Da Sundukai 720

Fashola Ya Ce Ma’aikatar Sa Ta Dawo Da Sundukai 720

170
0
Babatunde Raji Fashola, Ministan ma’aikatar Lantarki, Da Ayyuka Da Gidaje
Babatunde Raji Fashola, Ministan ma’aikatar Lantarki, Da Ayyuka Da Gidaje

Tsohon ministan ma’aikatar lantarki, da ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola,  ya ce a lokacin da ya shugabanci ma’aikatar a zangon farko na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya dawo da kimanin sundukai 720  ma’aikatar.

Karanta labaru masu Alaka: Ma’aikatu 3 Sun Yi Wa Fashola Ya Wa – Okorocha

Fashola ya bayyana hakan ne a lokacin da ake tantance shi a gaban majalisar dattawa don bashi mukamin minister a karo na biyu.

A cewar Fashola, sundukan 720 an karkatar da su ne bayan suna dauke da kayayyakin wutan latarki dan haka yayi kokarin ganin an dawo da su.

Sai dai a nasa bangaren  Sanata Rochas Okorocha ya kalubalanci Fashola,  inda yace ma’aikatu uku da aka bashi a baya sun yi masa yawa  dan haka da wuya ya sake samun su.