Tsohon ministan ma’aikatar lantarki, da ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola, ya ce a lokacin da ya shugabanci ma’aikatar a zangon farko na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya dawo da kimanin sundukai 720 ma’aikatar.
Karanta labaru masu Alaka: Ma’aikatu 3 Sun Yi Wa Fashola Ya Wa – Okorocha
Fashola ya bayyana hakan ne a lokacin da ake tantance shi a gaban majalisar dattawa don bashi mukamin minister a karo na biyu.
A cewar Fashola, sundukan 720 an karkatar da su ne bayan suna dauke da kayayyakin wutan latarki dan haka yayi kokarin ganin an dawo da su.
Sai dai a nasa bangaren Sanata Rochas Okorocha ya kalubalanci Fashola, inda yace ma’aikatu uku da aka bashi a baya sun yi masa yawa dan haka da wuya ya sake samun su.