Home Labaru Ahmad Lawal Ya Nada Melaye, Ndume, Shekarau, Da Goje

Ahmad Lawal Ya Nada Melaye, Ndume, Shekarau, Da Goje

735
0
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa

Majalisar dattawa ta fitar da sunayen wadanda za su shugabanci kwamitoci daban daban a majalisar.

Shugaban majalisar Ahmad Lawal, ya bayyana Sanata Ali Ndume a matsayin wanda zai shugabanci kwamitin kula da harkokin sojin kasa, sai Danjuma Goje, da zai shugabanci kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen ruwa, sannan Dino Melaye, ya jagoranci kwamitin kula da harkokin sufurin jirgin sama.

Karanta labaru Masu Alaka: Majalisa Za Ta Binciki Gwamnatocin Obasanjo Da ‘Yar Adua Da Jonathan Da Buhari

Sanata George Sekibo zai shugabanci kwamitin kula da harkokin sojin ruwa, Ibrahim Shekarau, zai shugabanci kwamitin kula da harkokin aikin gwamnati, yayin da Kabiru Gaya zai jagoranci kwamitin kula da harkokin hukumar zabe ta INEC, shi kuma Barau Jibrin ya shugabanci kwamitin kula da harkokin kasafin kudi.

Sauran wadanda su ka samu manyan kwamiti sun hada da Uba Sani, da Adedayo Adeyeye, da Ibikunle Amosun, da Bala Ibn Na’Allah, da Rochas Okorocha, da Aliyu Magatakarda Wamakko, da kuma Sabo Nakudu.