Home Labaru Ronaldo Ya Harzuka Magoya Bayan Sa

Ronaldo Ya Harzuka Magoya Bayan Sa

409
0

Masu sha’awar wasan kwallon kafa da ke cike da takaicin kin buga wasa da Cristiano Ronaldo ya yi a karawar sada zumunta da Juventus ta yi a Koriya ta Kudu sun harzuka kuma suna neman diyya.

An tsara cewa gwarzon dan wasan zai taka leda na tsawon minti 45 a karawar ta Juventus da kungiyar Koriyar ta K League All Stars, in ji wadanda suka shirya wasan amma sai Ronaldon ya zauna a benci kawai bai buga wasan ba.

Masu sha’awar dan wasan sun harzuka da suka ga ba shi da alamar shiga wasan, inda suka rika kiran sunan abokin hamayyar sa Lionel Messi suna yabon sa.

Wasu daga cikin ‘yan kallon a yanzu sun tunkari wani kamfanin lauyoyi a birnin Seoul, mai suna Myungan domin shigar da kara kan kin biya musu bukatar su da Ronaldon ya yi ta shiga wasan.

 Sunce suna neman a biya su diyya ta makudan kudade kan tikitin da suka saya da kamashon da aka samu na sayar da tikitin da kuma diyya kan bata musu rai da lamarin ya yi.